Facebook-Trump

Facebook ya dakatar da Trump shekaru biyu

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump MANDEL NGAN AFP/Archivos

Facebook ya dakatar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump na tsawon shekaru biyu bisa karya  wasu ka’idojin dandalin sada zumuntar a yayin harin da magoya bayansa suka kai ginin Capitol, lokacin da ‘yan majalisar Amurka ke tsaka da zamansu.

Talla

Dakatarwar ta fara aiki tun daga 7 ga watan Janairu, lokacin da kamfanin ya fara dakile sakwannin Trump na sai baba-ta-gani.

Sai dai a yanzu an rage tsawon lokacin haramcin zuwa shekaru biyu bayan a watan jiya Kwamitin Kula da Ka’idojin Hulda a Facebook ya caccaki dakatarwar ta sai baba-ta-gani.

Mista Trump dai ya caccaki matakin da Fecebook ya dauka a kansa, yana mai bayyana haka a matsayin cin fuska ga miliyoyin mutanen da suka  kada masa kuri’a a zaben shugabancin Amurka a bara.

Tuni Facebook ya yi wasu sauye-sauye a dokokinsa, inda ya ce, daga yanzu ba zai sake bai wa masu rike da madafun iko kariya ba muddin suka watsa sakwannin masu haddasa fitina.

Mataimakin Kamfanin Facebook, Nick Clegg ya bayyana cewa, koda shekaru biyun da aka yanke wa Trump sun cika, akwai yiwuwar tsawaita su muddin aka fahimci cewa, sakwanninsa ka iya ci gaba da haifar da barazanar wargaza zaman lafiyar al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.