Kungiyar G7 ta amince da shirin dokar harajin manyan kamfanoni

Ministocin kudi na kasashen da suka fito daga kungiyar G7
Ministocin kudi na kasashen da suka fito daga kungiyar G7 AFP - HENRY NICHOLLS

Kasashen kungiyar G7 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun amince da shirin dorawa manyan kamfanonin duniya harajin kashi 15 kamar yadda Amurka ta shirya makawa kamfanonin sadarwa da takwarorin su na wasu bangarori na daban saboda makudan kudaden da suke samu a matsayin riba.

Talla

Sakatariyar Baitulmalin Amurka Janet Yellen ta bayyana matukar farin cikin ta da matakin wanda tace zai taimaka wajen sanya harajin bai daya ga irin wadannan kamfanoni na duniya.

Shima kamfanin Facebook ya bayyana goyan bayan sa ga shirin duk da ganin cewar yana daya daga cikin wadanda matakin zai shafa, yayin da wasu kungiyoyi masu zaman kan suke cewa matakin yayi kadan.

Bayan kammala taron kwanaki biyu da ministocin kudaden kungiyar G7 suka gudanar a birnin London, sanarwar taron ta bayyana cewar za’a aiwatar da shirin ne daga kasa zuwa kasa.

Kasashen dake cikin kungiyar G7 sun hada da Birtaniya dake shugabancin kungiyar yanzu haka sai Canada da Faransa da Jamus da Italia da Japan da kuma Amurka.

Kungiyar tace zata kai wannan matsaya zuwa taron kungiyar G20 da zai gudana a watan Yuli domin samun goyan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.