Faransa-Mali

RFI na goyon bayan dan jaridar da ya yi watanni 2 a gun 'yan ta'adda

Daukacin ma'aikatan RFI na goyon bayan Olivier Dubois
Daukacin ma'aikatan RFI na goyon bayan Olivier Dubois © David Baché/RFI

Yau watanni biyu kenan da sace dan Jaridar kasar Faransa Olivier Dubios a arewacin kasar Mali. An dai kama shi ne a yankin Gao, inda ya shirya yin hira da Kungiyar taimaka wa addinin Islama da Musulmin dake alaka da kungiyar Al Qaeda a Arewacin Afirka. Tuni ya bayyana a faifan bidiyo inda ya ce kungiyar JNIM ce ta kama shi. RFI ta shiga cikin shirin bai wa dan Jaridar goyon baya wajen taimaka masa a Bamako da Paris.

Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraran sanarwar da RFI ta fitar game da Olivier Dubois

Sanarwar RFI kan Oliver Dubois

Shirin taimaka wa Olivier Dubois ya fara da kawo iyalansa da abokansa da sauran ‘yan Jaridu a Mali, inda Olivier Dubois ke zama da iyalansa tun daga shekarar 2015 har ma da Faransa.

Daga cikin taimakon, har da na Kungiyar dake kare hakkin yan Jaridu ta RSF da wadanda Olivier ke yi wa aiki da suka hada da Jaridun Liberation‘, ‘the Point‘, da ‘Jeune Afrique‘, da kafofin yada labaran ‘France Media Monde‘ da suka hada da RFI da France 24 da MCD da ma mutanen da aka taba garkuwa da su, yan Jaridu da wadanda ba yan  Jaridu ba.

Bukatar ita ce ganin Olivier Dubois ya koma cikin iyalansa cikin gagagwa, ta hanyar janyo hankalin duniya kan abin da ya faru a Faransa da kuma kasashen duniya.

Olivier Dubois dan jarida ne mai zaman kansa wanda yanayin yankin da yake aiki bai hana shi harkokin sa na bada labarai ba kamar yadda ya nuna a shekarun da suka gabata na zuwa tsakiyar Mali.

 Yan uwansa suma sun tabbatar da haka a tsarin sa na kwarewar aiki.

 Ya bar Gao da ke arewacin Mali ne ranar 8 ga watan Afrilu domin yin hira da shugaban kungiyar da ke Taimaka wa Musulunci da Musulmi JNIM da ke da alaka da AQMI wanda ke karkashin Iyad Ag Ghaly.

Iyalan Olivier Dubois da farko sun ki cewa komai, har zuwa lokacin da ya bayyana a faifan bidiyo ranar 4 ga watan Mayu inda shi Olivier Dubois da kansa ya bayyana cewar kungiyar JNIM ce ta kama shi, saboda haka babu shakku dangane da kama shi. Wannan ya sa aka bayyana gagarumin shirin hadin kai har zuwa lokacin da za’a sake shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.