WHO-Coronavirus

WHO na son a yi raba-daidai a maganin Korona

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus Christopher Black World Health Organization/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci masu sarrafa magungunan rigakafin cutar korona da su bai wa shirin Covax damar samar da maganin ko kuma bada rabin wadanda suke sarrafawa domin rabawaa daidai tsakanin kasashe masu arziki da matalauta.

Talla

Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya bukaci kamfanonin da ke sarrafa magungunan da su mayar da hankali kan shirin Covax da ke kokarin tara kudade domin samarwa kasashe matalauta maganin kyauta.

Tedros ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda kasashe matalauta suka gaza yi wa ma’aikatan lafiyarsu rigakafi  tare da dattijai da kuma mutanen da suka fi bukatar sa.

Wasu kasashe masu hali da suka sayi tarin maganin, bayan kammala yiwa wadanda suka fi bukatar allurar har sun fara yiwa yara kanana, yayin da sauran kasashen duniya ke neman maganin ruwa a jallo.

Tedros ya bayyana fatar ganin an yi wa akalla kashi 10 na al’umma duniya rigakafin nan da watan Satumba, yayin da ake saran yi wa kashi 30 nan da karshen shekara.

Shugaban hukumar ya ce wannan zai samu ne kawai idan aka samu karin allura miliyan 250 nan da Satumba da kuma wasu miliyan 100 tsakanin wannan wata na Yuni zuwa Yuli.

Tedros ya ce, shugabannin kungiyar kasashen G7 da suka fi karfin tattalin arziki na duniya za su gudanar da taronsu a karshen wannan mako, kuma wadannan kasashe guda 7 na da karfin da za su iya samarwa duniya maganin da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.