G7 - Tattalin Arziki

Biden ya sha alwashin karfafa alakar Amurka da Turai gabannin taron G7

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Nicholas Kamm AFP/File

Shugaban Amurka Joe Biden ya bar Washington domin fara ziyarar Turai wadda zata hada da halartar taron kungiyar G7 da kungiyar kasashen Turai da kungiyar NATO da kuma ganawa gaba da gaba da shugaban Rasha Vladimir Putin.

Talla

Kafin ya hau jirgi domin kama hanyar tafiyar sa a Washington, shugaba Joe Biden yace ganawar da za suyi da shugaba Vladimir Putin na Rasha da kasar China zata bashi damar jaddada danganta mai karfi dake gudana tsakanin Amurka da Turai.

Ziyarar shugaban zata fara da Birtaniya inda zai halarci taron kungiyar G7 a Cornish da kuma ganawa da Sarauniya Elizabeth ta biyu a Fadar Windsor, kafin daga bisani ya wuce zuwa Brussels inda zai halarci taron kungiyar tsaro ta NATO da na kungiyar kasashen Turai sannan ya karkare a Geneva inda zai gana da shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Yayin da duniya ke farfadowa daga annobar korona, shugaba Biden zai mayar da hankali ne kan sake dawo da jagorancin Amurka a fagen siyasar duniya.

Bayan inganta harkar samar da maganin rigakafi ga kasashe matalauta da farfado da tattalin arzikin kasashen duniya, Biden na fuskantar babban kalubalen hada kan kasashen duniya domin tinkarar kasashen Rasha da China.

A kasidar da ya rubuta da aka wallafa a Jaridar Washington Post kafin tafiyar sa, shugaba Joe Biden ya bayyana wannan tafiyar a matsayin mai matukar muhimmanci a wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.