Amurka-Corona

Amurka za ta rabawa matalautan kasashe rigakafin corona miliyan 500

Wasu alluran rigakafin corona.
Wasu alluran rigakafin corona. AP - Rahmat Gul

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kasar za ta sayi allurar rigakafin corona da Pfizer-BioNTech ke sarrafawa har guda milyan 500 don raba wa kasashen duniya.

Talla

A cewar Biden za a raba alluran milyan 200 a bana yayinda sauran milyan 300 za a raba su a shekara mai zuwa, duk dai a kokarin hada hannu don kawar da cutar ta covid-19 daga ban kasa.

Shugaba Biden zai sanar da hakan ne a hukumance a lokacin taron shugabannin kasashe 7 masu karfin tattalin arziki wato G7 da za a fara a gobe kamar dai yadda jaridun Washington Post da kuma New York Times suka ruwaito.

Amurka na cikin jerin kasashen da suka fi wahaltuwa daga cutar, ko da ya ke matakan da gwamnatin Biden ke dauka bayan shudewar ta Donald Trump da kuma rigakafin da kasar ke ci gaba da yiwa jama'arta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.