AMURKA-KORONA

Amurka zata rabawa kasashe 100 maganin korona kyauta - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden yana gabatar da jawabi
Shugaban Amurka Joe Biden yana gabatar da jawabi AP - Patrick Semansky

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana shirin gwamnatin sa na baiwa kasashe matalauta 100 na duniya taimakon allurar rigakafin cutar korona miliyan dubu 500 samfurin Pfizer domin ganin sun kare jama’ar su daga illar cutar.

Talla

Biden wanda ke ziyarar Birtaniya ya bayyana haka ne bayan ganawa da Firaminista Boris Johnson, inda yake cewa hakkin Amurka ce ta taimakawa kasashen duniya musamman marasa karfi wajen ceto rayukan jama’a.

Biden yace wannan mataki ne mai dimbin tarihi na cinikin maganin mafi yawa da kuma bada gudumawar sa ga wasu kasashen duniya wanda ba‘a taba yi ba a tarihin duniya.

Shugaban yace Amurka ta bada gudumawa fiye da duk wata kasa cikin rumbun COVAX dake taimakawa kasashe matalauta maganin rigakafin a fadin duniya, yayin da ya tabbatar da cewar suna da isasshen maganin rigakafin da kowanne BaAmurke zai samu, abinda ya sa suka bayyana shirin bada gudumawar allura miliyan 80 daga cikin wanda suke da shi a cikin gida yanzu haka.

Biden yace taimakawa kasashen duniya shawo kann annobar zai taimaka wajen kare lafiyar Amurkawa, kuma Amurka zata cigaba da rike matsayin ta na jagorancin duniya.

Shugaban ya kuma jaddada cewar babu wani sharadi da suka gindayawa kasashen duniya 100 da zasu ci gajiyar kyautar allurar maganin Pfizer da zasu raba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI