WHO-Muhalli

Kasashen Duniya za su samar da makamashi marar gurbata muhalli

An cimma matakin ne tsakanin fannonin lafiya na fasaha da na samar da makamashi a kokarin ceto Duniya.
An cimma matakin ne tsakanin fannonin lafiya na fasaha da na samar da makamashi a kokarin ceto Duniya. © Paola Barisani/AP

Shugabannin kasashen duniya fiye da 20 da ministocin lafiya da na samar da makamashi, da kuma shugabannin hukumomin kasa da kasa, gami da kungiyoyin fararen hula, sun amince da sabbin tsare-tsaren bunkasa fannonin kula da lafiya da samar da makamashi don amfanin al’ummar duniya.

Talla

Shugabannin sun cimma wannan matsaya ce yayin taron da suka yi a karkashin jagorancin shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebereyesus matakin da ya share fagen fara aiwatar da matakan inganta fasahohin makamashin da masana’antu ke amfani da shi da kuma na girki, gami da inganta tsarin kula da lafiya zuwa na zamani a fadin duniya.

Hasashen hukumar lafiya ta duniya WHO da ta wallafa a baya bayan nan, ya nuna cewar a shekarar 2019 kadai, mutane akalla biliyan 2 da miliyan 600 ne suka shiga hatsarin shakar gurbatacciyar iska a fadin duniya, sakamakon rashin wadatar tsaftataccen makamashin girki da wanda masana’antu ke amfani da shi, matsalar da ke haddasa mutuwar mutane akalla milyan 4 duk shekara, dalilin fama da cutukan da suka hada da na matsalar numfashi mai alaka da Huhu, kansa, mutuwar barin jiki, da kuma numonia.

A wani rahoton kuma, hukumar ta WHO ta kiyasta cewar har yanzu mutane akalla biliyan 1 ne basa samun ingantaccen tsarin kula da lafiya a sassan duniya ciki har da matsalar karancin wutar lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.