Myanmar-MDD

Rikici ya tsananta a Myanmar- MDD

Sojojin Myanmar sun murkushe masu zanga-zangar adawa da kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi
Sojojin Myanmar sun murkushe masu zanga-zangar adawa da kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi STR AFP/File

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, rikici na tsananta a sassan Myanmar, yayin da ta yi gargadin cewa, kasar ta tsunduma cikin bala’in keta hakkin bil’adama tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 1 ga watan Fabairu.

Talla

A yayin da take mayar da martani kan yadda sojojin Myanmar suka mamaye sassan kasar, Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya  Michelle Bachelet ta bukaci gaggauta dakatar da rikicin kasar domin hana salwantar rayuka.

A cikin sanarwar da ta fitar, Bachelet ta ce, a cikin watanni hudu kacal, Myanmar ta sauya daga tafarkin demokuradiya zuwa yanayi na ibtila’in keta hakkin dan adam.

Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta dora laifin rikicin kasar kan sojojin da suka kwace ragamar shugabancin kasar daga halastacciyar gwamnati.

Tun ranar 1 ga watan Fabairun da ya gabata ne, Myanmar ta tsunduma cikin rikici bayan janar-janar na soji sun kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.

Majalisar Dinkin Duniyar ta yi laka’ri da wani sahihin rahoto da ke nuna cewa, akalla fararen hula 860 aka kashe a sanadiyar murkushewar da sojoi suka yi wa masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.