G7 - China

G7 ta cimma matsaya kan shirin gasa da China wajen mu'amala da kasashe matalauta

Shugabannin kasashen G7 dake taro a Birtaniya, 12 ga watan Yunin 2021
Shugabannin kasashen G7 dake taro a Birtaniya, 12 ga watan Yunin 2021 © France24

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 sun amince da wani shirin nuna adawa ga shirin kasar China da ke taimakawa kasashe matalauta wajen inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa.

Talla

Matakin kasashen na zuwa ne bayan Shugaba Joe Biden na Amurka, da takwarorinsa sun gana  a taron da ke wakana a Kudancin Burtaniya, inda suka tattauna matakin kawo karshen gasa da kasar China, tare da shan alwashin samar da ababen more rayuwa ga matalautan kasashe da kuma kasashe masu matsakaicin karfin tattalin arziki.

Gasa da China

Kasashen duniya dai na ci gaba da sukar shirin kasar China da take dorawa kananan kasashe dimbin basuka, yayin da suke ganin zai yi wuya kasashen da ke amfana da kasar su iya sauke basussukan da ake bin su.

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta G7 dai, sun sha alwashin hada karfi da karfe don samar da daruruwan biliyoyin kayayyakin more rayuwa ga kasashe masu karamin karfi da masu matsakaitan kudaden shiga.

Kungiyar ta G7 ta ce kasashen za su hada gwiwa don ganin cewa tallafin da za su bawa kasashe matalauta ya amfane su yadda ya kamata.

Annobar korona

A wani bangaren kuma Birtaniyya ta yaba da yarjejeniyar G7, inda shugabannin suka yi alkawarin magance annobar Covid-19 da ta salwantar da rayukan miliyoyin mutane da kuma lalata tattalin arziki.

Kungiyar kasashen ta G7 da suka kunshi kasashen Burtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da kuma Amurka - za su sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance ranar Lahadi, inda ake sa ran za su bayyana muradan da ake kokarin cimmawa dangane da batun shawo kan matsalar annobar Corona, da kuma yadda za su tallafawa kasashe matalauta, sabanin yadda kasar China ke tallafa musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.