G7

Kasashen G7 na cigaba da ganawa a Birtaniya

Shugabannin kasashen kungiyar G7 da kawayensu a Birtaniya.
Shugabannin kasashen kungiyar G7 da kawayensu a Birtaniya. © Patrick Semansky/Pool via REUTERS

Shugabannin kasashen kungiyar G7 dake cigaba da taro a Birtaniya na shirin bayyana sabbin tsare-tsaren kawo karshen annobar Korona da kuma dakile bullar wasu cutukan makamantanta a nan gaba.

Talla

A wannan Asabar aka shiga rana ta biyu a taron na G7 na keke da keke karo na farko cikin kusan shekaru 2, yau din ne kuma ake sa ran shugabannin kasashen Australia, afrika ta Kudu, Korea ta Kudu da kuma India domin tattaunawa kan wasu jerin manufofin kasashen ketare da kuma matsalar sauyin yanayi.

Gabannin soma taron daga ranar Juma’a da zai shafe  kwanaki 3 yana gudana a Birtaniya, kasashen na kungiyar G7 da suka hada da Jamus, Italiya Faransa, Birtaniya, Canada, Japan da kuma Amurka sun ce shirin samar da tallafin na alluran rigakafin cutar Koronar, dama ce muhimmiya ta kawo karshen annobar da kawo yanzu ta lakume rayukan mutane fiye da miliyan 3 ad dubu 700.

Ba ya ga batun yaki da annobar ta Korona da kuma daidaito wajen rabon alluran rigakafin cutar tsakanin kasashe masu arziki da matalauta, taron kasashen na G7 zai kuma tattauna kan kudurin yankawa manyan kamfanonin fasahohin zamani na Apple, Amazon, Facebook da kuma Google, biyan tarar kashi 15 na jumillar ribar da suke samu a shekara, kamar yadda shugaban Amurka Joe Biden ya nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI