Majalisar Dinkin Duniya

Kwamitin tsaron MDD ya zabi sabbin manbobi

Zauren kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
Zauren kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya. © REUTERS/Mike Segar/File Photo

Jami’an Diflomasiyya sun ce an zabi kasashen Brazil, Hadaddiyar Daular Larabawa, Albania, Gabon da kuma Ghana a matsayin manbobin da ba na dindindin ba a kwamitin tsaron majalisar dinin duniya daga shekarar 2022 mai kamawa zuwa ta 2023.

Talla

Kasashen za su fara aikin zama cikin kwamitin tsaron ne daga watan janairun sabuwar shekara, inda za su maye guraben kasashen Vietnam, Estonia, da kuma tsibiran Saint Vincent da Grenadines.

Jami’an dilomasiyyar kasashe 193 dake zauren majalisar dinkin duniya ne suka kada kuri’un zaben sabbin mabobin kwamitin sulhun majalisar da ba na dindindin ba, inda Brazil ta lashe kuri’u181, Hadaddiyar Daular Larabawa 179, Albania 175, Gabon 183, yayin da Ghana ta samu 185.

Kwamitin tsaro ko na sulhun majalisar dinkin duniya dai ya kunshi jumillar kasashe 15, biyar daga cikinsu manbobin ne na dindindin da suka hada da Faransa, Rasha, Birtaniya, China da kuma Amurka. Yayin da ragowar kasashe 10 ke kasancewa manbobin wucin gadi da za suke karba karba da wasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.