FARANSA-MALI

Sanarwar France Medias Monde dangane da kashe Baye Ag Bakabo

Ofishin France Media Monde
Ofishin France Media Monde © /www.lalettre.pro

Sakamakon kashe kwamandan Yan ta’addan Mali Baye  Ag Bakabo da sojojin Faransa suka yi kafofin yada labaran Faransa a karkashin France Medias Monde sun fitar da sanarwa kamar haka.

Talla

Kafofin yada labaran Faransa na France Medias Monde sun bayyana samun labarin kisan Baye Ag Bakabo wanda ya kama da kuma kashe wakilan RFI guda 2 Ghislaine Duppont da Claude Verlon ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2013 a Kidal dake Mali, kuma suna dakon binciken shari’a da ake cigaba da yi akan kashe Yan Jaridun su guda 2 domin bayyana abin tashin hankalin da ya faru da zai kaiga kama ‘yayan kungiyar da kuma sauran kwamandodin su da masu taimaka musu domin fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI