Aghanistan - Taliban

Tsaron ofisoshin jakadanci da filayen jiragen sama na kan Afghanistan - Taliban

Ana ci gabada fargaba dangane da tsaron ma'aitakan kasashen waje bayan kammala ficewar dakarun Amurka da NATO a kasar Afghanistan
Ana ci gabada fargaba dangane da tsaron ma'aitakan kasashen waje bayan kammala ficewar dakarun Amurka da NATO a kasar Afghanistan WAKIL KOHSAR AFP/File

Kungiyar Taliban tace kada Sojojin kasashen waje su yi 'fatan' ci gaba da kasancewa a Afghanistan bayan Amurka da NATO sun gama janye sojojinsu, tana mai gargadi danagene da tsaron ofisoshin jakadanci da filayen jiragen saman da ke zama alhakin dakarun Afghanistan.

Talla

Hakan na zuwa ne yayin da jami'an diflomasiyyar kasashen yamma da jami'an soji ke shirin tattaunawa kan yadda za a samar da tsaro ga duk wani farar hula da zai ci gaba da kasancewa a kasar nan gaba.

Sojin Turkiya

Rahotanni sun ce Turkiyya ta ce a shirye take ta ci gaba da kasancewa da dakarunta a Afghanistan domin kare filin jirgin saman Kabul, babbar hanyar fita ga jami’an diflomasiyyar kasashen yamma da ma’aikatan jin kai.

Fargaba

Kasar Amurka na cikin matakan karshe na kammala janye dakarunta da na NATO, kafin ranar 11 ga watan Satumba, dai-dai lokacin cika shekaru ashirin bayan da suka mamaye Afghanistan tare da kawar da Taliban.

Wannan na zuwa ne sakamakon fargaba da wasu kasashen duniya ke yi dangane da tsaron ma'aitakan kasashen su dake Aghanistan bayan kammala ficewar dakarun Amurka da NATO a kasar Afghanistan, sakakon barazar komen Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.