Syria - Ta'addanci

Tagwayen hare-hare sun kashe mutane 13 a Syria

Asibitin Al Shifa da farmaki ya rusa a garin Afrin dake kasar Syria.
Asibitin Al Shifa da farmaki ya rusa a garin Afrin dake kasar Syria. © PressTV/Anadolu news agency

Akalla mutane 13 ciki har da ma’aikatan lafiya 2 sun rasa rayukansu yayin da wasu 27 jikkata, a tagwayen hare-haren da aka kai kan garin Afrin dake arewacin Syria. da manyan makaman Atillery.

Talla

Bayanai sun ce harin na farko ya afkawa bangaren gidajen fararen hula ne, a yayin da na biyu kuma ya fada kan wani Asibiti dake garin Afrin.

Kawo yanzu dai ba kai ga tantance wanda ya kai farmakin ba, harin da aka ce ya fito ne daga bangaren yankin dake karkashin sojojin gwamnatin Syria da kawayensu mayakan Kurdawa.

Har aynzu dai garin Afrin dake arewacin Syria na karkashin ikon mayakan sa kan da kasar Turkiya ke marawa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.