Yemen - Bakin Haure

An tsamo gawarwakin bakin haure 25 a ruwar Yemen

Wani kwalekwale a mashigin ruwar Amurka
Wani kwalekwale a mashigin ruwar Amurka - US COAST GUARD/AFP

An tsamo gawarwakin wasu bakin haure 25 daga Yemen a ranar Litinin bayan kwale-kwalen da ke dauke da su ya kife da mutane sama da 200 da ke cikinsa. A cewar rahotanni, wasu Masunta ne suka gano gawarwakin lokacin da suke aikin kama kifi a cikin ruwan Ras al-Ara a lardin Lahij da ke kudancin kasar, yankin da aka alakanta da sansanin safarar mutane.

Talla

Jirgin ruwan ya kife ne kwanaki biyu da suka gabata wanda ke dauke da tsakanin mutane 160 zuwa 200, inda ake laluben sauran mutanen da suka nitse a kogin.

Hukumar Kula da ‘yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa wani kwale-kwale ya nitse a yankin amma har yanzu ana kokarin gano bayanan musabbabin faruwar lamarin.

Duk da yakin da ake yi a Yemen da ya haifar da tsananin talauci, bakin haure na ci gaba da tafiya can da nufin tsallakawa Saudi Arabiya da sauran makwabtan kasashe masu arzikin mai da nufin samun aiki me gwabi.

Masuntan sun ce wadanda abin ya rutsa da su, wanda aka gano a mashigar Bab al-Mandab da ta raba Djibouti da Yemen, da alama 'yan asalin Afirka ne.

'Yan ci-rani galibi kan tsinci kansu a cikin kasar ta Yemen, wacce ta fada cikin mawuyacin halin bayan rikicin shekaru shida.

Yankin bakin teku na Ras al-Ara na daga cikin wuraren da masu fataucin mutane suka fi addabar su.

A watannin baya-bayan nan, bakin haure da dama sun mutu a mashigar Bab al-Mandab, wadda babbar hanya ce ta cinikayyar kasa da kasa amma kuma ta fataucin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.