JAMUS-KISA

Ana tuhumar wata mata da kashe 'yayan ta guda 5 a Jamus

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel REUTERS - ANNEGRET HILSE

Wata mata mai shekaru 28 a kasar Jamus yau ta gurfana a gaban kotu domin amsa tuhumar da ake mata akan dalilin da ya sa ta kashe ‘yayan cikin ta guda 5 daga cikin guda 6 da ta haifa.

Talla

Matar wadda aka bayyana sunan ta a matsayin Christiane K. na fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai idan kotu ta tabbatar da laifi akan ta a shari’ar da ake mata a Wuppertal dake Yammacin Jamus.

An dai gano gawarwakin yara mata guda 3 masu shekaru 1 da 2 da 3 da kuma yara maza 2 masu shekaru 6 da 8 a gidan ta dake birnin Solingen ranar 3 ga watan Satumbar bara.

Yan sanda sun ce an samu gawarwakin yaran guda 5 lullube a cikin tawul an shimfidar da su kwance akan gadon su.

Masu gabatar da kara na zargin cewar mahaifiyar ta su tayi amfani da guba cikin abincin karyawar da ta basu domin sanya su suyi bacci kafin ta sanya su a cikin ruwan wankar da ta hallaka su.

Bayan aikata kisan Christiane tayi kokarin kashe kan ta wajen jefa kan ta a gaban jirgin kasa lokacin da yake tafiya a tashar Duesseldorf amma sai aka gaggauta ceto ta ba tare da ta samu raunin da zai mata illa ba.

‘Dan ta na 6 mai shekaru 11 ya tsallake rijiya da baya domin lokacin da ta kashe ‘yan uwan sa shi yana makaranta.

Matar da ake zargin taki amincewa da tuhumar da ake mata inda take cewa wani mutum rufe da fuska ne ya shiga gidan ya kashe yaran, amma masu gabatar da kara sun ce babu wata shaidar dake tabbatar da haka.

Masu gabatar da karar sun ce mahaifiyar tayi amfani da rashin wayon yaran wajen hallaka su baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.