G7 - Tattalin Arziki - Sauyin Yanayi

Kasashen G7 sun sha alwashin kawo karshen annobar Korona

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Birtaniya Boris Johnson, yayin taron kasashen kungiyar G7.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Birtaniya Boris Johnson, yayin taron kasashen kungiyar G7. © AFP - LUDOVIC MARIN

Shugabannin kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, sun lashi takobin fara rarraba rigakafin Covid-19 har guda biliyan 1, yayin da suka bayyana aniyarsu ta kara kaimi wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi.

Talla

Duk da cewa, kasashen na gungun G7 sun ce, za su rarraba alluran rigakafin biliyan 1 ga kasashen duniya matalauta, masu fafutuka na cewa, adadin ya yi karanci matuka, ganin cewa, a kalla ana bukatar rigakafin ne har biliyan 11 a matalautan kasashen domin kawo karshen wannan annoba  wadda ta lakume rayukan mutane kusan miliyan 4 tare da gurgunta tattalin arzikin duniya.

Kazalika, an caccaki gungun na G7 dangane da alkawuransa na isar da karin kayyakin agaji ga kasashe matalauta masu tsananin fama da tasirin sauyin yanayi, inda ake cewa, agajin ya yi karanci  kuma an jinkirta shi, ganin cewa, yana zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaban sashin yaki da rashin daidaiton tsare-tsare na Kungiyar Agaji ta Oxfam, Max Lawson ya bayyana cewa, wannan taron na G7 za a ci gaba da tuna shi da rashin kayatarwa.

A cewar Lawson, taron ya gaza tunkarar kalubalen da ake fama da su a yanzu kuma mafi muni a cikin karni guda musamman a bangaren kiwon lafiya da kuma sauyin yanayi wanda ke yin ta’adi ga wannan duniyar da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI