US-CORONAVIRUS

Adadin mutanen da suka mutu a Amurka sun zarce dubu 600

Shugaban Amurka Joe Biden wajen taron kungiyar NATO
Shugaban Amurka Joe Biden wajen taron kungiyar NATO AP - Patrick Semansky

Adadin mutanen da annobar korona ta kashe a kasar Amurka sun zarce dubu 600 kamar yadda Jami’ar Johns Hopkins dake tattara alkaluman masu fama da cutar ta sanar.

Talla

Wannan adadi da hukumomin Amurka suka gabatar ya dada tabbatar da jagorancin kasar a matsayi ta farko cikin jerin kasashen da cutar korona tafi yiwa illa a gaban kasashen Brazil da India abinda ya sa shugaba Joe Biden ya bukaci al’ummar kasar da su cigaba da rungumar shirin rigakafi.

Biden yace abin takaici rayukan mutane na cigaba da salwanta duk da raguwar mutanen dake mutuwa kowacce rana sabanin yadda aka saba gani a watanni baya.

Shugaban ya aike da sakon ta’aziyya ga daukacin Amurkawan da suka rasa ‘yan uwan su sakamakon wannan annoba wanda yace tayi sanadiyar mutuwar mutanen da suka zarce yakin duniya na farko da na biyu da kuma yakin Vietnam baki daya.

Biden yace har yanzu akwai sauran aiki a gaban su wajen ganin sun shawo kan annobar, saboda haka babu lokacin da za’a bata wajen yaki da ita.

Hukumomin lafiyar kasar sun ce ya zuwa wannan lokaci sama da kashi 52 na Amurkawa ko kuma sama da miliyan 172 ne kawai suka karbi allurar rigakafi sau guda a cikin kasar daga cikin magunguna guda 3 da aka amince da sahihancin su.

Shugaba Biden ya gindaya sharadin yiwa Amurkawa sama da kashi 70 allurar rigakafin nan da ranar ‘yancin kan Amurka ta 4 ga watan Yuli, amma masana na ganin cimma matsayin na da wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.