Amurka-Ta'addanci

Amurka ta kaddamar da shirin yaki da ayyukan ta'addanci a cikin gida

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Patrick Semansky

Gwamnatin Amurka ta kaddamar da wani shirin yakar ayyukan ta’addanci a cikin gida, wanda ke matsayin guda cikin kudirin shugaba Joe Biden na kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta ta fuskar kaiwa mutanen da basu ji basu gani ba farmaki musamman daga bangaren masu ra’ayin kin jinin bakaken fata.

Talla

Shirin yakar ayyukan ta’addancin a cikin Amurka mai kunshe da rukunnai 4 wanda zai bayar da damar tofa albarkacin baki na da nufin sauya tunanin jama’a game da yunkurin daukar matakin aikata ta’addancin a cikin gida sabanin amfani da tsauraran matakai.

Wani babban jami’in gwamnatin Joe Biden da AFP ba ta bayyana sunansa ba, ya ce ayyukan ta’addancin cikin gida na matsayin babban kalubalen da ke barazana ga Amurka da Amurkawa cikin 2021.

Jami’in ya ce ayyukan ta’addancin masu alaka da wariyar launin fata ko kuma banbancin kabila, na ci gaba da tsananta a Amurkan duk da kasancewarta kasar da ke tattare da miliyoyin mabanbantan kabilu da addinai, yayinda a bangare guda ta’addancin masu adawa da gwamnati da na masu kalubalantar yawan bakake a madafun iko suma ke ci gaba da karuwa.

Karkashin shirin na Joe Biden da ke fatan sassauta matsalolin ta’addancin a cikin gida, masu alaka da wariya zai taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan ‘yan kasar da kuma gamsar da su kan muhimmancin zaman tare baya ga bayar da kariya ga wadanda ke fuskantar barazanar ta’addanci, duk da hakan bisa sahale wanzuwar dokokin tofa albarkacin baki.

Kafin kankamar shirin, gwamnatin ta Amurka ta bukaci, bayyanawa ko kuma shigar da bayanai kan makamantan ta’addancin a kowanne mataki wanda zai bayar da damar daukar matakan da suka dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.