AMURKA-TALLAFI

Attajirar Amurka zata raba Dala biliyan 2 da rabi kyauta

MacKenzie Scott
MacKenzie Scott © Bloomberg.com

Daya daga cikin mata attajiran da suka fi kudi a duniya MacKenzie Scott dake Amurka ta bayyana shirin raba kudin da ya kai Dala biliyan 2 da miliyan 700 kyauta ga bangaren samar da ilimi da kula da al’umma da kuma kungiyoyi masu zaman kan su.

Talla

MacKenzie wadda tsohuwar matar mutumin da ya mallaki kamfanin Amazon Jeff Bezos ne ta bayyaan shirin gabatar da wani sashe na dukiyar ta ta daga cikin da ta samu wajen rabuwar da suka yi da mijinta kuma kungiyoyin da zasu amfana da shirin sun kai 286.

Wannan sanarwar itace irin ta ta 3 da matar wadda dukiyar da ta mallaka ta kai Dala biliyan 59 ta gabatar bayan irin wannan taimako na kudin da ya Dala biliyan 6 da ta bayar ga daruruwan kungiyoyi da makarantu a fadin Amurka.

MacKenzie taki amincewa da bukatar kafa Gidauniya ta kan ta wadda zata dinga gudanar da irin wadannan ayyukan, inda ta dogara da masu bata shawara wajen gano kungiyoyi da hukumomin dake bukatar taimako tana kai musu dauki.

A sakon da ta aike, Attajiran tace mutanen dake fafutukar yaki da banbanci na bukatar gurbi wajen hanyar da zasu kawo sauyi a rayuwar su.

MacKenzie tace ita da masu bata shawara na kokarin bada wani kaso na dukiyar da ta mallaka domin samar da sauyi da zummar ganin dukiya bata takaita ga wasu ‘yan tsirarun mutane ba.

Attajiran tace babu wani sharadi da za’a gindayawa kungiyoyi ko makarantu ko al’ummar da zasu amfana da gidauniyar wajen gudanar da harkokin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI