Coronavirus-G7

Covid-19-Tallafin G7 ga kasashe matalauta ya yi kadan

Shugabannin kasashen G7
Shugabannin kasashen G7 Ludovic MARIN AFP/File

Hukumomin kiwon lafiya na duniya da suka hada da WHO sun bayyana cewa, adadin alluran rigakafin Covid-19 biliyan 1 da gungun G7 ya yi alkawarin bai wa kasashe matalauta, ya yi kadan matuka, yayin da kwararru ke cewa, ana bukatar alluran har guda bilyan 11 a halin yanzu don shawo kan annobar a duniya.

Talla

Kungiyar G7 ta kasashen da suka fi karfin tattalin arziki, ta yi alkawarin samar da rigakafin Korona guda biliyan 1  ga kasashe matalauta a karshen mako, amma tana shan caccaka saboda nuna son-kai wajen mallakar rigakafin.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, sun yi lale marhabin da sanarwar G7 ta samar da alluran, amma suna bukatar karin rigafin cikin gaggawa a cewarsa.

Kasashen duniya mawadata na ci gaba da morewa daidaiton al’amura saboda tarin rigakafin da suka mallaka, amma har yanzu, ana ci gaba da fama da karancin alluran a mafi yawan sassan duniya.

Akwai gagarumar tazara tsakanin kasashen na G7 da sauran kasashen ya-ku-bayi wajen mallakar alluran rigakafin, inda Bankin Duniya ya bayyana tazarar tsakanin 73 da 1.

Ya zuwa yanzu, an isar da alluran rigakfin guda miliyan 85 ga kasashen duniya 131 a karkashin wani  shiri na Majalisar Dinkin Duniya, amma wannan adadi ya yi karanci sosai.

G7 ya ce, yana da aniyar yi wa daukacin duniya rigakafin Covid-19 nan da shekara mai zuwa, amma halayyarsa ya nuna cewa, ya fi mayar da hankali kan kare ‘yancin mallakar rigakafin a cewar Kungiyar Agaji ta Oxfam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI