Amurka-Turai

Ganawa mai cike da tarihi tsakanin Biden da shugabannin Turai

Shugaban Amurka Joe Biden da wasu shugabannin Turai
Shugaban Amurka Joe Biden da wasu shugabannin Turai AP - Jacques Witt

A yau talata, shugaban Amurka Joe Biden na doguwar tattaunawa da shugabannin kasashen Turrai 27 a gaban shugaban majalisar Turai Charles Michel da kuma shugabar hukumar Yankin Ursula ven der Leyen.

Talla

Wannan dai zai kasance karon farko tun 2017 da za a yi irin wannan ganawa kai tsaye tsakanin shugabannin, wadda aka shirya da zummar warware sabanin da ya samo asali a tsakaninsu tun zuwa Donald Trump kan karagar mulki.

Taron zai yi kokarin warware sabanin kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen na Turai, wanda ya haddasa karin haraji a kan hajojin da suke musayar kasuwanci a tsakaninsu.

Hakazalika akwai wata yarjejeniyar shekaru 17 da ta bukaci a kawo karshen takaddama tsakanin kamfanin kera jiragen Boeing na Amurka da takwaransa na Turai wato Airbus, yarjejeniyar da wa’adin aikinta zai kawo karshe a ranar 11 ga watan yulin wannan shekara.

A lokacin mulkin shugaba Trump, Amurka ta lafta haraji kan karafan da yankin Turai ke shigar wa a kasar, rikicin da bangarorin biyu za su tattauna da nufin kawo karshensa kafin karshen watan disamba mai zuwa.

A lokacin taron, Shugaba Biden zai yi kokarin samun goyon bayan Turai don daukar mataki kan China, duk da cewa Jamus da Faransa na da bambancin ra’ayi da Amurka kan batutuwan da suka shafi kasar ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.