Amurka - Rasha

Babu hasashen fahimtar juna a ganawar Biden da Putin - Masana

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin AFP - ERIC BARADAT,PAVEL GOLOVKIN

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin na ganawa Laraban nan, a haduwarsu ta farko tun bayan da Biden ya hau karagar mulki, to sai dai babu tsammanin cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu masu banbancin ra’ayi.

Talla

Shugabannin biyu sun amince suyi ganawar a gefen tafkin Geneva, inda ake fatan su samu fahimtar juna da bude wani sabon babi na maido da hulda tsakanin kasashen biyu dake samun rarrabuwar kawuna a bangarori da dama.

Amurka da Rasha na takaddama kan batutuwa da dama, kama daga batun takaita mallakar makamai da kutse ta hanyar intanet, da batun kutsen zabe da kuma lamuran da suka shafi Ukraine.

Babu fatan samun nasara

Wani babban jami'in Amurka ya fadawa manema labarai a cikin jirgin Air Force One yayin da Biden ya tashi zuwa Geneva, yana mai cewa ana sa ran za su tattauna na tsawon awanni hudu ko biyar da misalin karfe 11: 30 agogon GMT, to sai dai yace, basa tsammanin wani sauyi.

Shugaban Amurka Joe Biden yayin da yake sauka a jirgin saman Airfoce one na kasar Amurka domin ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Geneva, 16 ga watan Yuni 2021.
Shugaban Amurka Joe Biden yayin da yake sauka a jirgin saman Airfoce one na kasar Amurka domin ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Geneva, 16 ga watan Yuni 2021. AP - Martial Trezzini

Yayin da shima mai baiwa shugana Putin shawara kan harkokin kasahen waje  Yuru Ushakove yace "Bashi da tabbas ko za’a cimma matsya da kuma kulla wata yarjejeniya ba."

Shugaban Rasha Vladimir Putin yayin tattaunawa da tashar MBC a Moscow ranar 11 ga watan Yuni 2021.
Shugaban Rasha Vladimir Putin yayin tattaunawa da tashar MBC a Moscow ranar 11 ga watan Yuni 2021. Maxim Blinov SPUTNIK/AFP/File

Tsamin dangantaka

Dangantaka ta tabarbare tsawon shekaru tsakanin kasashen biyu, musamman mamayar da Rasha ta yi wa yankin Crimea dake Ukraine a shekarar 2014, Amurka ta kuma zargi Rasha da shiga yakin Syria a shekarar 2015 - wanda Moscow ta musanta – sai kuma batun tsoma bakinta a zaben 2016 wanda ya kawo Donald Trump Fadar White House.

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin Jim WATSON, Grigory DUKOR AFP/File

Kasashen biyu sun kuma nunawa juna yatsa a karkashin jagorancin Biden na baya-bayan nan a watan Maris, lokacin da kira Putin “mai kisan kai”, matakin da ya sa Rasha ta sake kiran jakadanta da ke Washington komawa gida, yayin da itama Amurka ta kira jakadanta a watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI