Rasha-Amurka

Ganawata da Biden ta yi armashi- Putin

Shugaban Amurka Joe Biden tare da Vladimir Putin na Rasha
Shugaban Amurka Joe Biden tare da Vladimir Putin na Rasha AP - Alexander Zemlianichenko

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, ganawarsa da takwaransa na Amurka Joe Biden ta yi armashi, yayin da kasashen biyu suka amince kan wasu batutuwa da suka hada da mayar da jakadunsu da zummar inganta alakarsu da kuma musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Gabanin zaman irinsa na farko a tarihi na ranar Laraba, shugabannin biyu yi musahafa da juna a birnin Geneva, inda suka nuna alamu na annashuwa da kuma niyar cimma matsaya.

Shugabannin biyu sun gaisa da juna bayan sun tsaya tare da mai masaukinsu kuma shugaban Switzerland, Guy Parmelin a harabar dandalin shakatawa na La Grange, inda suka rika kallon Tafkin Geneva.

Kazalika tattaunawarsu ta tsawon sa'o'i biyar ta mayar da hankali kan batun kutsen shafukan intanet da katsalandan a zabuka da keta hakkin bil’adama da sauran wasu batutuwa masu cike da sarkakiya.

Joe Biden da Vladimir Putin sun yi ganawar ce a wani kasaitaccen  dakin adana littafai da ke birnin Geneva.
Joe Biden da Vladimir Putin sun yi ganawar ce a wani kasaitaccen dakin adana littafai da ke birnin Geneva. REUTERS - KEVIN LAMARQUE

Biden da Putin da suka zauna gefe da gefe a wani  kasaitaccen dakin adana littafai, sanye da kwallon taswirar duniya a tsakaninsu, ga kuma tutocin kasashensu a bayansu, sun yi musayar zance kafin daga bisani a sallami ‘yan jaridar da suka yi musu rakiya cikin dakin.

Bayan kammala ganawar ce, Putin ya halarci taron manema labarai domin karbar tambayoyi.

Shugaba Putin dai ya mika godiyarsa ga Biden bisa shirya wannan haduwa a tsakaninsu.

Putin ya ce,  alakar Amurka da Rasha na tattare da wasu batutuwa da dama da ke bukatar zama na musamman don tattaunawa a kansu, yana mai fatan wannan zama zai haifar da da-mai-ido.

Shi kuwa Biden cikin murmushi  cewa ya yi, zaman keke da keke shi ya fi dacewa a kodayaushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.