ICC

Sabon mai shigar da kara na ICC na da jan aiki

Karim Khan, sabon mai shigar da kara a Kotun Duniya ta ICC
Karim Khan, sabon mai shigar da kara a Kotun Duniya ta ICC SABAH ARAR AFP

Karim Khan na Biritaniya ya kama aiki a matsayin sabon mai shigar da kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC inda ake sa ran zai fara ne da manyan kararrakin da ke gaban kotun, ciki kuwa har da batun rikicin da ke wakana tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Talla

Sabon mai shigar da karar mai shekaru 51, ya maye gurbin Fatou Bensouda ta Gambiya, wacce ta fadada tsare-tsaren kotun ta ICC a tsawon shekaru tara da ta yi tana jagoranci, ciki har da wanke tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo.

Khan ya sha alwashin farfado da martabar kotun da ke dauke da dimbin manyan korafe-korafe a gabanta, duk da nasarorin da ta samu a baya.

Khan a baya ya jagoranci wani bincike na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan aikata laifuka daga kungiyar masu da’awar jihadi a kotun ta ICC.

Fatou Bensouda ta  musanta zargin da ake yi wa kotun na musguna wa kasashen Afrika.
Fatou Bensouda ta musanta zargin da ake yi wa kotun na musguna wa kasashen Afrika. Bas Czerwinski/Pool via REUTERS/File Photo

Ana ganin tsohuwar mai shigar da karar kotun wato Bensouda ta bar shi da ayyuka masu zafi ciki kuwa har da batun bincike kan yadda ake yaki da ta’ammali da  miyagun kwayoyi a kasar Philippines.

Baya ga wannan, akwai binciken da ake yi wa Amurka da aikata laifukan yaki a Afghanistan, sai kuma rikicin da ke wakana tsakanin Isra’ila da Falasɗinu.

Lauyan na Burtaniya zai kuma kalubalanci adawar manyan kasashe da suka ki shiga kotun ta ICC, irinsu Amurka da Isra'ila da China da kuma Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.