WHO-LAFIYA

Adadin mutanen dake mutuwa sakamakon kunar bakin wake ya karu - WHO

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus Christopher Black World Health Organization/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana kunar bakin wake a matsayin hanyar da aka fi amfani da ita wajen kashe jama’a a fadin duniya kowacce shekara.

Talla

Wani rahotan binciken Hukumar Lafiya da aka wallafa ya bayyana cewar kowacce shekara mutanen dake mutuwa sakamakon kunar bakin wake ya zarce na masu fama da cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro ko sankarar nonon mata.

Hukumar tace a shekarar 2019 mutane sama da dubu 700 suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake, abinda ya sa ta gabatar da hanyar taimakawa kasashen duniya shawo kan kisan.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus yace ba zasu kauda kan su akan kisan da ake ta hanyar kunar bakin wake ba, musamman a wannan lokaci da annobar korona tayi matukar illa ga mutanen duniya wajen sanya su rasa ayyukan su da hanyoyin samun kudaden su abubuwan dake iya haifar da matsalar.

Alkaluman Hukumar sun bayyana cewar matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 29 na mataki na 4 cikin jerin mutanen da ake samu suna mutuwa ta hanyar kunar bakin waken bayan hadarin mota da cutar tarin fuka da kuma rikici tsakanin jama’a.

Hukumar tace binciken ta ya nuna banbancin da ake samu a matsalar daga kasa zuwa kasa da kuma yanki zuwa wani yankin tare da tsakanin maza da mata.

Rahotan yace adadin mazan dake mutuwa sakamakon kunar bakin wake ya ribanya na mata, yayin da kuma aka fi samun matsalar a Afirka fiye da Turai da kuma kasashen dake Kudu Maso Gabashin Asia, sai kuma Gabashin Meditereniya inda matsalar bata girma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.