Majalisar Dinkin Duniya - 'Yan Gudun Hijira

Yawan 'yan gudun hijira a fadin duniya ya haura miliyan 82 - MDD

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijira daga Kabilar Rohingya da suke tserewa tashe-tashen hankula a kasarsu ta Myanmar.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijira daga Kabilar Rohingya da suke tserewa tashe-tashen hankula a kasarsu ta Myanmar. © REUTERS/Danish Siddiqui

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsanantar tasirin annobar Korona bai hana hauhawar adadin miliyoyin mutanen da yaki da sauran tashe-tashen hankula da masifu ke tilastawa yin gudun hijira ba.

Talla

Cikin sabon rahoton da ta fitar, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR ta ce yanzu haka adadin mutanen da suka tagayyara bayan rasa muhallansu sakamakon yake-yake, tashin hankali na rikice-rikice da zalunci ya miliyan 82 da dubu 400 a fadin duniya.

Rahoton dai ya nuna cewar yawan mutanen dake gudun hijira a duniya ya ninka cikin shekaru 10 kacal, daga mutane miliyan 40 a shekarar 2011 zuwa miliyan 82 da dubu 400 a karshen shekarar 2020, wadanda mafi akasarinsu ke sansanonin da aka kafa a kasashen su na asali.

Sansanin 'yan gudun hijira na Khazer dake kasar Iraki dauke da mutanen da rikicin IS ya raba da muhallansu a birnin Mosul. 23/11/ 2016.
Sansanin 'yan gudun hijira na Khazer dake kasar Iraki dauke da mutanen da rikicin IS ya raba da muhallansu a birnin Mosul. 23/11/ 2016. © REUTERS/Mohammed Salem

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yake-yaken da ake yi a kasashen Syria, Afghanistan, Somalia da Yemen a matsayin dalilan dake kan gaba wajen janyowa karuwar miliyoyin ‘yan gudun hijirar a sassan duniya, yayinda kuma sabbin tashe-tashen hankulan kasashen Habasha da Mozambique ke barazanar sake dagula lamurra.

Kididdigar Majalisar ta kuma bayyana cewar yanzu haka akwai ‘yan kasar Venezuela kadai kusan miliyan 4 da suka tsere daga kasashensu saboda rikicin siyasa da na tattalin arziki, wadanda har yanzu hukumomi bas u yi musu rijistar zama ‘yan gudun hijira ba, yayin da kuma a gefe guda adadin Falasdinawa da suka tsere daga yankinsu ya kai miliyan 5 da dubu 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.