Iran

Ebrahim Raisi ya lashe zaben kasar Iran

Iranians line up to vote at a polling station in the Hosseinyeh Ershad mosque in the capital Tehran
Iranians line up to vote at a polling station in the Hosseinyeh Ershad mosque in the capital Tehran ATTA KENARE AFP

Hukumar zaben Iran ta sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a jiya, inda aka fafata tsakanin ‘yan takara 4, ciki har da Ebrahim Raisi fitaccen malamin addini zai maye gurbin shugaba mai barin gado Hassan Rouhani, Ebrahim Raisi ya lashen zaben da kusan kashi 62 cikin dari na kuri’u da aka kada.

Talla

A jiya Juma’a sai da hukumar zaben Iran ta kara sa’o’I biyu kan lokacin da aka kayyade za a rufe rumfunan zabe,matakin da wasu ke dangantawa da karancin fitar jama’a da akalla kashi 40 zuwa 50.

Ebrahim Raïssi sabon shugaban kasar Iran a wata rufar zabe a kasar ta Iran
Ebrahim Raïssi sabon shugaban kasar Iran a wata rufar zabe a kasar ta Iran VIA REUTERS - WANA NEWS AGENCY

Yan lokuta da fitar da sakamakon zaben kasar,manyan kasashe da dama ne yanzu haka suka soma bayyana ra’ayoyin su tareda isar da fata na gari  ga sabon Shugaban kasar da ake kyautata zaton  zai shifuda sabon babbe dangane da batuttuwan da suka shafi batun tattaunawa na Nukiliyar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI