Isra'ila - Falasdinawa

Falasdinawa sun soke shirin karbar alluran rigakafin Korona daga Isra'ila

Alluran rigakafin cutar Korona.
Alluran rigakafin cutar Korona. AP - Francisco Seco

Gwamnatin yankin Falasdinu ta soke shirin karbar tallafin alluran rigakafin Korona da Isra’ila ke shirin mika mata, bayan da bayanai suka nuna aikin magungunan na gaf da karewa sabanin lokacin da aka sanar da fari.

Talla

Ma’aikatar yankin na Falasdinu ta ce tun da farko gwamnatin Isra’ila ta shaida musu cewa alluran rigakafin na Korona miliyan 1 da dubu 400 za su daina aiki ne a cikin watan Yuli ko Agusta, amma daga bisani binciken kwararrunsu ya nuna aikin alluran zai kawo karshe a cikin watan Yunin da muke.

Kawo yanzu dai ofishin sabon fira ministan Isra’ila Naftali Bennet ba ice komai kan lamarin ba.

Isra’ila na shan caccaka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam kan rashin taimakawa yankin falasdinu wajen samun isassun alluran rigakafin Korona a birnin gaza da kuma Gabar Yamma Da Kogin Jordan, duk da cewa, Isra’ilar na daga cikin kasashen da suka aiwatar da shirin yiwa al’ummominsu rigakafin cutar cikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI