Yemen - Houthi

Sabon fada ya barke tsakanin sojojin Yemen da mayakan Houthi

Sabon fada tsakanin mayakan 'yan tawayen Houthi da dakarun Yemen yayin sanadin mutuwar mayaka fiye da 40.
Sabon fada tsakanin mayakan 'yan tawayen Houthi da dakarun Yemen yayin sanadin mutuwar mayaka fiye da 40. © Getty Images

Sabon fada ya barke tsakanin sojojin Yemen da ‘yan tawayen Houthi dake kokarin kwace iko da birnin Marib birni mafi girma dake karkashin ikon gwamnati a arewacin kasar bayan shafe shekaru 6 suna fafatawa.

Talla

Bayanai sun ce fadan da ake gwabzawa tun daga jiya Asabar yayi sanadin mutuwar mayaka akalla 47 ciki har da 16 dake bangaren dakarun gwamnatin kasar ta Yemen.

‘Yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran dai sun dade suna fafutukar kwace iko da birnin na Marib da kuma filayen hakar danyen man dake zagayensa.

Sabon fadan ya barke ne bayan gazawar yunkurin cimma matsayar kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, bayan lafawar fadan da suke gwabzawa da tsawon makwanni.

Yanzu haka dai miliyoyin mutane ke cikin bala’in yunwa gami da tagayyara a kasar Yemen tun bayan barkewar yaki a shekarar 2014, tsakanin dakarun Saudiya da ‘yan tawayen Houthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.