Belarus-Turai

Kasashen duniya sun yi wa Belarus rubdugu

Shugaban Belarus Alexandre Loukachenko
Shugaban Belarus Alexandre Loukachenko AP - Sergei Shelega

Birtaniya ta bi sahun Amurka da Tarayyar Turai da kuma Canada wajen sanya sabbin takunkumai kan Belarus, abin da ke matayin martani ga matakin shugaba Alexandre Lukashenko na kamewa tare da daure dan jaridar da ke adawa da gwamnatinsa.

Talla

Tun farko Ministocin Wajen Kungiyar EU suka fara daukar matakin sanya takunkuman biyo bayan taronsu na makon jiya, inda takunkuman suka fara aiki kan Belarus a ranar Litinin, yayin da kasashen na Birtaniya da Canada da kuma Amurka suka mara musu baya.

Tuni dai takunkuman suka shafi manyan jami’an gwamnatin Belarus wanda ya kai ga kulle ilahirin asusun ajiyarsu na ketare tare da haramta musu bulaguro.

Birtaniya ta fitar da sanarwar nata takunkuman ne na daban da EU da kuma Amurka wadanda dukkaninsu suka shafi shi kansa shugaba Lukashenko da kuma manyan mukarraban gwamnatinsa.

Dukkanin sanarwar da kasashen na Birtaniya da Canada da Amuka baya ga EU, sun ja kunnen Belarus kan hadarin da ke tattare da take hakkin dan adam.

Alaka ta kara tsami tsakanin Belarus da manyan kasashen duniya ne bayan karkatar da jirgin Ryanair da Lukashenko ya yi a watan jiya don kame matashin dan jaridar da ya yi kaurin suna a caccakar gwamnatinsa.

A cewar hadakar sanarwar kasashen fiye da 30, sun ce Lukashenko ya jefa rayukan fasinjan jirgin a hadari bayan tilasta musu sauka ta hanyar tsorata su da sanya bom a cikin jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.