WHO-Kwallon Kafa

WHO ta gargadi Turai kan sassauta dokar Korona saboda Kwallo

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus Christopher Black World Health Organization/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana damuwa kan yadda kasashen Turai ke sassauta dokar yaki da cutar Korona saboda wasannin kwallon kafa a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Talla

WHO ta lura cewa, wannan sassauacin dokar ya haddasa hauhawar  masu kamuwa da cutar Coronavirus, yayin da babban Diraktan Hukumar a Turai  Robb Butler ya ce, sun damu da sassauta wannan doka a wasu kasashen nahiyar  da ke karbar bakwancin gasar.

Butler ya ce, sun lura cewa, ana samun karuwar ‘yan kallo a wasu filayen da ake gudanar da gasar ta cin kofin kasashen Turai.

Koda yake Hukumar Lafiyar ta Duniya ba ta ambaci wani birni ko kuma kasa  kai tsaye, amma a Talatar nan ne, Birtaniya ta sanar cewa, sama da ‘yan kallo dubu 60 ne za su shiga filin wasa na Wembley da ke birnin London domin kallon wasannin matakin gab da na karshe  da kuma wasan karshe a gasar.

Tun da farko dai, kimanin ‘yan kallo dubu 40 aka shirya cewa, za su halarci wasannin karshen, amma gwamnatin Birtaniya ta kara adadinsu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da annobar  Korona ke tsananta a wasu kasashen na Turai da ke karbar bakwancin gasar ta Euro 2020 a cewar  Butler.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.