Iran ta koka kan matakin Amurka na toshe mata kafofin yada labarai

Face au rejet des candidatures de trois poids lourds de la scène politique iranienne, le principal candidat conservateur, l'ayatollah Ebrahim Raissi, chef de la Justice, a affirmé lui-même qu'il menait des consultations pour tenter d'obtenir la qualification de certains candidats pour que l'élection soit plus compétitive.
Face au rejet des candidatures de trois poids lourds de la scène politique iranienne, le principal candidat conservateur, l'ayatollah Ebrahim Raissi, chef de la Justice, a affirmé lui-même qu'il menait des consultations pour tenter d'obtenir la qualification de certains candidats pour que l'élection soit plus compétitive. AFP - HO

Amurka ta kulle wasu gungun kafofin yada labaran Iran 2 tare da wani daban na ‘yan tawayen Huthi a Yemen bayan da ta zarge su da yada labaran karya da farfaganda, matakin da ke zuwa kasa da sa’o’i 48 bayan zababben shugaban kasar ya ja tunga game da shirin tattaunawarsa da Joe Biden da nufin ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Talla

Gungun kafafofin yada labaran mallakin Iran da suka kunshi Press TV mai yada labarai da harshen turanci da kuma Al-Alam na harshen labarabci, dukkaninsu na da kananun shafukan labarai 33 a karkashinsu.

Dukkanin shafukan yada labaran 33 da ke karkashin gungun biyu da kuma wadanda ke karkashin Al-Masirah TV ta ‘yan tawayen Huthi na nuna alamun babu damar shiga tare da karin bayanin cewa hukumar FBI da takwararta ta kasuwanci na Amurkan sun kulle shafukan saboda farfaganda da kuma yada labaran karya da Iran ke amfani da su waje aiwatarwa.

Tuni dai Iran din ta zargi Amurka da take dokokin fadar albarkacin baki, yayinda ta yi gargadin cewa matakin na Amurka bai isa ya tirsasata shiga tattaunawar nukiliyarta da ke kokarin dawo da Washington din cikinta ba.

Mahmoud Baezi da ke matsayin daraktan fadar shugaban Iran ya ce kasar za ta ci gaba da daukar dukkan matakan caccakar Amurka game da rufe shafukan yada labaran 33

Har zuwa yanzu dai Amurka ba ta yi karin bayani game da matakin kulle shafukan labaran na Iran ciki har da wadanda ke yada shirye-shiryensu a Iraqi da Yemen ba, yayinda maimagana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Ned Price ya ki amsa tambayar manema labarai kan batun maimakon haka sai ya umarci da su tuntubi bangaren shari’a don karin bayani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI