Amurka-Corona

Rigakafin Pfizer da Moderna na haddasa kumburin zuciya ga matasa- Amurka

Wasu matasa bayan karbar alluran rigakafin corona na Pfizer.
Wasu matasa bayan karbar alluran rigakafin corona na Pfizer. Pablo VIGNALI adhoc/AFP

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka ta sake gargadi kan karuwar wadanda ke gamuwa da matsalar kumburin zuciya musamman ga matasan da suka karbi rigakafin covid-19 samfurin Moderna da na hadakar Pfizer da BioNTech.

Talla

Tuni dai hukumar ke shirin gudanar da wani taron tattaunawa tsakaninta da hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar don lalubo hanyoyin magance matsalar, bayan karuwar matasan da ke gamuwa da matsalar zuciyar a sassan kasar.

Hukumar ta ce hadarin gamuwa da matalar zuciyar ga matasan da suka karbi allurar rigakafin ta covid-19 samfurin Pfizer na matsayin kashi 1.4 yayinda na Moderna ke matsayin kashi 4.2.

Baya ga Amurkan hukumomin lafiya da dama a sassan Duniya na ci gaba da bincike don gano ko kamfononin da suka samar da samfurin rigakafin na Pfizer da BioNTech da kuma Modern ana amfani da fasahar mRNA da ke haddasa kumburin zuciya ko akasin haka.

Duk da cewa hukumar yaki da cutuka masu yaduwar ta Amurka ta ce galibin matasan da kan hadu da matsalar kumburin zuciyar bayan karbar alluran rigakafin na warkewa cikin hanzari, amma hukumar kula da ingancin abinci da magungunan ta ce akwai bukatar gudanar da bincike kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.