Canada-Katolika

Canada ta gano kaburbura marasa rijista 751 a gab da makarantar Katolika

Wasu kaburbura mabiya addinin Kirista.
Wasu kaburbura mabiya addinin Kirista. Michael DANTAS AFP/File

Canada ta gano kaburbura 751 da basa dauke da alama a kusa da tsohuwar makarantar kwana ta mabiya darikar Katlika da ke yammacin Canada, wanda kuma shi ne karo na biyu da kasar ke gano irin wannan cikin kasa da wata guda.

Talla

Shugaban wata kabilar lardin Cowessess, Cadmus Delorme ya bayyana gano karburburan, wanda ke kara tabbatar da irin bala’in da yara ‘yan makarantar kabilun asalin Canada suka sha fama da su shekaru da dama karkashin kulawar magabatan majami’ar ta Katlika.

Cadmus ya ce,  akwai alamun wasu daga cikin karburburan na dauke da alamu a baya kafin a cire daga bisani, inda ya ce ko da hakan ya tabbata, y ana matsayin babban laifi ga dokokin kasar Canada da ta wajabta samar da alama ga kowanne kabari don sanin duk wani da ke kwance a kasa.

Ko a watan jiya sai da hukumomin kasar suka sanar da gano kaburburan dalibai 215 a kusa da wata Makarantar kwana ita ma dai mallakin mabiya darikar ta Katlika, lamarin da ya tayar da hankalin kasar baki daya, wanda ya kai ga kira ga Shugaban darikar ta Duniya Fafaroma Francis da kuma majami’arsa kan su nemi gafara kan cin zarafi da tashe-tashen hankula baya ga take hakkin dan adam din da aka yi a makarantun da ke karkashinsu.

Akwai dai zargin da ke nuna shugabanin da ke kula da makarantun da ke karkashin majami’ar ta katlika da cin zarafin kananan yara da fyade tare da kisan sama da dalibai dubu 4 a cikin kasar ta Canada tare da raba kimanin Amurkawa 150 da iyayensu da kuma harsuna da kuma al’adunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.