Amurka - Floyd

Hukuncin daurin shekaru 22 ya hau kan dan sandan da ya kashe George Floyd

Tsohon dan sandan Amurka a birnin Minneapolis Derek Chauvin a kotu bisa tuhumar kashe George Floyd bakar fata.
Tsohon dan sandan Amurka a birnin Minneapolis Derek Chauvin a kotu bisa tuhumar kashe George Floyd bakar fata. AFP - ALEX LEDERMAN

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 22 da rabi kan tsohon dan sandan Amurka Drek Chauvin da aka samu da laifin kashe George Floyd bakar fata a birnin Minneapolis.

Talla

Yayin zartas da hukuncin, Alkali Peter Cahill ya ce babu alaka tsakanin matsayar kotu kan hukuncin daurin da batun tausayi, ko ra’ayin mutane.

Tun da fari dai daurin shekaru 30 masu gabatar kara suka nemi a zartas kan tsohon dan sanda Chauvin saboda kashe George Floyd da yayi.

A karkashin doka dai Chauvin ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 30 kan tuhumar kisan gillar da aka yi masa, sai dai dokokin jihar Minnesota inda yake aiki sun fayyace kamata yayi tsohon dan sandan ya fuskanci hukuncin shekaru 12 da rabi, la’akari da cewar hukuma ba ta taba samunsa da aikata wani laifi ba.

Masu zanga-zanga a birnin Minneapolis na jihar Minnesota kan kin jinin cin zalin da 'yan sanda ke yiwa mutane a Amurka
Masu zanga-zanga a birnin Minneapolis na jihar Minnesota kan kin jinin cin zalin da 'yan sanda ke yiwa mutane a Amurka Kerem Yucel AFP/Archivos

Cikin watan Mayun shekarar 2020 kisan George Flyd ya janyo barkewar zanga-zanga a wasu biranen Amurka da suka hada da New York, Washington, Atlanta, Los Angeles da Minneapolis dake jihar Minnesota, inda boren ya samo asali.

Wani bidiyo da ya karade kafafen Intanet ya nuna yadda dan sanda derek Chauvin ya taka wuyan bakar fatar da gwiwarsa tsawon mintuna, wanda daga bisani ya mutu sakamakon rashin shakar iska duk da cewar Floyd ya nemi bashi damar numfasawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.