Amurka-Iran

Lokaci na kurewa Iran game da yarjejeniyar Nukiliya - Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. REUTERS - POOL

Amurka da Faransa sun gargadi Iran kan yadda lokaci ke kokarin kure mata dangane da yunkurin ceto yarjejeniyar nukiliyar da ke tsakaninta da manyan kasashen Duniya, inda suka bayyana fargaba kan yiwuwar karuwar ayyukan samar da makamin Nukiliyar daga Iran idan har aka gaza cimma jituwa a tattaunawar.

Talla

Yayin wata ziyara irinta ta farko da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ke kai wa Faransa da ke bayyana fatar dinke barakar da ke tsakanin kasar da takwarorinta na Turai karkashin jagorancin shugaba Joe Biden biyo bayan tarnakin da suka fuskanta yayin mulkin Donald Trump, Blinken ya ce kasarsa na son goyon bayan Turai wajen daidaita yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

Yarjejeniyar wadda Trump ya cire Amurka a 2018, bayan da Barrack Obama ya jagoranci kullata a 2015, Blinken ya nanata bukatar Biden ta dawo da Amurka cikinta sai dai ya nanata gargadi kan yadda Tehran ke ci gaba da bunkasa yawan makamashin Uranium din da ta ke tacewa, wanda ke matsayin babbar hanyar samar da makamin.

A kalaman Blinken bayan ganawarsa da Emmanuel Macron, fatarsu ya iya gushewa idan har sabon zababben shugaban kasar ta Iran ya ki amincewa da ci gaba da tattaunawar da kasar ta faro a Vienna cikin watannin baya-bayan nan.

A cewar Blinken ana gab da kaiwa wata gaba da zai yiwa Iran din matukar wahala ta iya dawowa cikin yarjejeniyar ta JCPOA.

Bayaga Faransar da Amurka manyan kasashen Duniya da suka kunshi Birtaniya da Jamus da Rasha da kuma Chine ne ke jagorantar kulla yarjejeniyar da Iran inda Emmanuel Macron ke cewa suna fatan Iran ta dauki matakin karshe na komawa cikin yarjejeniyar tare da warware ayyukan da ta kulla karkashin shirin samar da nukiliyar bayan fara bijirewa dokokin yarjejeniyar a 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.