Najeriya - Kwayoyi

Yawan 'yan kwaya a Najeriya zai kai miliyan 20 nan da 2030 - MDD

Wani dan kwaya yayin kokarin yiwa kansa allurar gusar da hankali.
Wani dan kwaya yayin kokarin yiwa kansa allurar gusar da hankali. © REUTERS

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake sa ido kan tu’ammuli da miyagun kwayoyi gami da laifuka masu alaka da su UNODC, ya ce ‘yan Najeriya fiye da miliyan 14 da dubu 300 ne suka zaman 'yan kwaya bayan sha na’u’ikan kwayoyi daban daban a shekarar 2020.

Talla

Kididdigar ta bayyana cewa kimanin kashi 5.5 cikin 100 na yawan al’ummar Najeriya tsakanin masu shekaru 15 zuwa 64 sun yi tu’ammuli da akalla na’u’in kwaya guda a shekarar da ta gabata.

Wadannan alkaluma na kunshe cikin rahoton da Majalisai Dinkin Duniya ke fitarwa duk shekara kan yadda ake sha da kuma fasakaurin miyagun kwayoyi a fadin duniya.

Rahoton ya bayyana annobar Korona a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa karuwar shan miyagun kwayoyi tsakanin mutane la’akari da dokokin kullen da suka shafe tsawon lokaci a ciki, bayan matakin hana zirga-zirgar jama’ar da hukumomi suka dauka domin dakile yaduwar cutar.

Miyagun kwayoyi da yawansu ya kai ton 10, yayin kone su da jami'an hana fasaurin kwayoyin suka yi a jihar Kano dake Najeriya.
Miyagun kwayoyi da yawansu ya kai ton 10, yayin kone su da jami'an hana fasaurin kwayoyin suka yi a jihar Kano dake Najeriya. ©AMINU ABUBAKAR

Wani hasashe Da Majalisar Dinkin Duniyar tayi ya ce adadin masu shan miyagun kwayoyi a Najeriya zai karu zuwa mutane miliyan 20 nan da shekarar 2030.

A shekarar da ta gabata kadai dai mutane miliyan 257 suka sha nau’ikan miyagun kwayoyi daban daban a fadin duniya, yayinda wasu miliyan 36 cikinsu miliyan 3 a Najeriya ke fama da cutukan tabin kwakwalwa saboda muggan kwayoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.