Duniya - Coronavirus

Sabon nau’in Korona mafi hatsari ya bazu zuwa kasashe 85

Sabon nau'in cutar Korona na Delta ya haifar da fargaba kan yiwuwar sake barkewar annobar zango na 3.
Sabon nau'in cutar Korona na Delta ya haifar da fargaba kan yiwuwar sake barkewar annobar zango na 3. REUTERS - Phil Noble

Kasashe da dama sun soma daukar matakan dakile sabon nau’in cutar Korona na Delta mai saurin yaduwa da ya samo asali daga kasar India.

Talla

Kawo yanzu hukumomin lafiya sun tabbatar da bullar sabon nau’in Koronar a kasashe akalla 85, abinda ya haifar da fargaba kan yiwuwar fuskantar wani sabon zango na sake barkewar annobar karo na 3, duk da nasarar da aka cimma ta dakile ta a kasashe da dama bayan yiwa miliyoyin mutane alluran rigakafi.

Kwararru dai sun tabbatar da cewa nau’in Koronar na Delta shi ne mafi hatsari daga cikin dukkanin nau’ikan cutar da suka bayyana.

A Bangladesh, gwamnati ta sanar da kafa dokar kulle a daukacin kasar daga gobe Litinin saboda bullar nau’in Koronar na Delta,  yayin da a Australia dokar hana fitar tsawon makwanni 2 da ta shafi akalla mutane miliyan 5 ta soma aiki a birnin Sydney da zummar dakile yaduwar cutar.

Kawo yanzu annobar Korona ta halaka mutane kusan miliyan 4 a fadin duniya, tun bayan soma bulla daga birnin Wuhan na kasar China a watan Disambar shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.