Syria-Amurka

Amurka ta nemi kawayenta su kwashe jama'arsu daga Syria don murkushe IS

Wani yanki da ke karkashin kulawar Kurdawa a Syria.
Wani yanki da ke karkashin kulawar Kurdawa a Syria. Delil SOULEIMAN AFP/File

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kara matsin lamba ga kasashe aminan kasar kan su fara aikin kwashe jama'arsu da aynzu haka ke tsare a Syria a wani yunkuri na hanasu shiga kungiyar ta'addanci ta IS, ya na mai gargadin cewa ba za a ci gaba da rike su a Syria na har abada ba.

Talla

Blinken ya yi wannan kiran ne yayin ganawa da kawancen kasashen mambobi 83 na kawo karshen kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a duniya, a wani taro da suka gudanar a birnin Rome na kasar Italiya, inda suka yi kira da a mai da hankali sosai ga barazanar mayaka masu ikirarin jihadi a Afirka.

Wani kiyasin Amurka ya nuna akwai mayakan IS  kimanin dubu 10 da suka fito daga kasashe daban-daban dake tsare a hannun mayakan Kurdawa dake taimakawa kawancen kasashen yamma a arewacin Syria.

Blinkin ya ce, "Amurka na ci gaba da kira ga kasashe – masamman na kawancen - da su dawo da su gida, domin gyara musu hali, ko gurfanar da wadanda suka cancanci hukunci.

Faransa da Birtaniya dake matsayin manyan aminan Amurka, na yin dari-dari dangane da kiraye-kirayen dawo da ‘yan kasarsu gida, wanda tun gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.