Covid-19-Rigakafi

Kasashen Duniya sun yi amfani da alluran rigakafin covid-19 biliyan 3

Wasu alluran rigakafin Covid-19.
Wasu alluran rigakafin Covid-19. AP - Rafiq Maqbool

Wasu alkaluma na nuna yadda kasashen Duniya suka yiwa al’ummominsu amfani da alluran rigakafin covid-19 fiye da biliyan 3 tun bayan samar da alluran a kokarin yaki da annobar zuwa yanzu, dai dai lokacin da nau’in cutar da ake kira Delta ke barazana ga Duniya.

Talla

Wannan alkaluma na biliyoyin mutane da suka karbi rigakafin na covid-19, ya zo dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da zafafa musamman nau’in Delta wadda masana ke cewa tafi barazana ga mutanen da ke da karancin shekaru sabanin nau’ikan baya da suka fi barazana ga wadanda shekarunsu suka daata.

Zuwa yanzu mutanen da cutar ta kashe sun kai miliyan 3 da dubu dari 9 duk da ya ke wasu manyan kasashe sun yi nasarar shawo kanta tare da daidaita al’amura a kasashensu ta hanyar bayar da alluran rigakafin ga kaso mai yawa na jama’arsu, ciki har da Amurka a kan gaba, a bangare guda kuma sabuwar nau’in cutar wadda aka fara ganin bullarta a India ke ci gaba da barazana ga Duniya.

Yanzu haka nau’in cutar da aka kira da Delta na ci gaba da yaduwa a Rasha wanda ya kai ga kwantar da mutane dubu 151 a asibitoci yayinda alkaluman wadanda cutar ke kashewa kowacce rana ya kai kololuwa a wani yanayi da kasar ba ta taba gani ba.

Haka zalika tuni wasu birane suka dawo da dokokin takaita walwala, ciki har da Australia da Sydney bayan da masana ke ci gaba da jan hankali game da yiwuwar tarukan da Duniya ke gudanarwa a yanzu su kara yada cutar ciki har da gasar Euro da kuma Olympics da ke tafe.

Alkaluman da kamfanin dillancin labaran Faransa ya hada ya ce kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Isra’ila su ne kan gaba a jerin wadanda suka yiwa kashi 79 cikin dari na al’ummarsu rigakafin, yayinda matalautan kasashje ke baya, matakin da ya janyo hankalin ministocin wajen kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da suka nemi hada hannu don samar da wadatattun alluran da nufin kammala yakar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.