TikTok ya goge asusun kananan yara miliyan 7 saboda saba ka'ida

Tambarin kamfanin TikTok.
Tambarin kamfanin TikTok. Lionel BONAVENTURE AFP/File

Kamfanin da ke kula da dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da goge asusun mabiyansa fiye da miliyan 7 wadanda shekarunsu ya yi karanci galibinsu ‘yan kasa da 13 a Duniya saboda saba ka'idoji ciki har da yada bidiyon badala.

Talla

Kamfanin na TikTok mallakin ‘yan China wanda aka kaddamar a 2016 ya samu karbuwa ne sakamakon yadda ya ke saukaka nadar bidiyo tare da yada shi cikin sauki, inda a 2020 ya ke da mabiya biliyan 1 duk fadin Duniya da kaso mai yawa na fiye da mutane miliyan 100 a Amurka.

TikTok wanda ko cikin watanni ukun farkon shekarar nan sai da ya janye bidiyon da basu kamata ba har miliyan 62 saboda karya dokoki, ya ce kashi 80 na masu asusun hada bidiyon da kuma yadashi matasa ne da shekarunsu ya fara daga 12 zuwa 24.

A cewar TikTok matakin zaftare masu asusun da mutum miliyan 7 na da nasaba da yada bidiyon batsa, ko na kalaman batanci ko cin mutunci ko kuma haddasa rikici, wanda galibi yara ne ke dorawa wadanda shekarunsu ya fara daga 13 zuwa kasa.

Dandalin na TikTok da ke matsayin mafi saurin bunkasa tsakanin takwarorinsu na sada zumunta, ya ce akwai tanade tanade ga yaran da shekarunsu bai haura 12 a Duniya ba wadanda ke amfani da kafar, wanda kuma ke aiki a wasu kasashe ciki har da Amurka, yayinda kuma ma’aikatansa ke sanya ido tare da goge duk wani asusu da ya saba doka.

Kamfanin ya ce baya ga asusun kananan yaran miliyan 7 akwai kuma wasu asusu kusan miliyan 4 na daban da suma aka goge saboda yada bidiyon da bai kamata ba.

A watan jiya ne shugaba Joe Biden ya sauya hukuncin tsohon shugaban Amurka Donald Trump na tilastawa kamfanin ko dai ya daina aiki a Amurka ko kuma ya sayar da kamfanin ga 'yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.