Amurka-China

Amurka ta damu kan yadda China ke kara makamai

Wani nau'in makami a China
Wani nau'in makami a China AP - Andy Wong

Amurka ta nuna damuwarta kan yadda China ke kokarin ci gaba da aikin inganta makami mai linzami, tana mai kira ga Beijing da ta amince da tattaunawar da za a shirya don gudun yaduwar makamai a duniya.

Talla

A cewar Amurkar, shiga tattaunawa da kasashen duniya game da batun samar da makami mai linzami da kuma hadarin da ke tattare da kirkirar sa barkatai zai taimaka wajen fahimtar juna tsakanin kasashen.

Ko a makon da ya gabata, sai da wata jarida a Amurka ta bankado rahoton cewa, China na samar da wasu sinadaran hada makamai masu linzami har sama da dari da 19, kuma ma har ta fara gwajin su a yankin saharar kasar Yemen.

A cewar rahoton China na sane da dokokin kasa da kasa game da kera irin wadannan makamai, amma ta yi gaban kanta wajen ci gaba da kerawa duk da hadarin da hakan ke tattare da shi.

Amurka ta tabbatar cewa fahimtar juna tsakaninta da China za ta ta’allaka ne kadai idan China ta amince ta zauna kan teburin sulhu don tattauna batun samar da makami mai linzamin da kuma gwajin sa.

Sannan Amurka ta kuma koka kan yadda China ke ikirarin cewa, tana cikin kasashen da aka sahalewa mallakar makamin nukiliya, amma kuma ta ke nuna halin ganganci game da mallakar makamai masu linzami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.