Amurka-Ruftawar bene

Mutane 60 sun mutu a ruftawar ginin Amurka

Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin zakulo mutanen da ginin ya rufta da su a Florida
Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin zakulo mutanen da ginin ya rufta da su a Florida Giorgio VIERA AFP

Mahukuta a Amurka sun ce mutane 60 ne suka rasa rayukansu a ginin nan mai hawa 12 da ya rufta ranar 24 ga watan jiya a jihar Florida.

Talla

Har yanzu akwai sauran mutane fiye da 80 da ba a ji duriyarsu ba tun bayan bacewarsu jim kadan da aukuwar ibtila'in, yayin da ake fargabar mutuwarsu baki daya.

Babu mutum ko guda da aka ceto da ransa tun lokacin da jami'an agaji suka fara aikin laluben masu sauran numfashi a karkashin buraguzan ginin.

Hukumomin kasar na ci gaba da gudanar da bincike da zummar gano musabbabin aukuwar ruftawar ginin.

Shi dai wannan bene an gina  shi ne kimanin shekaru 40 da suka gabata, kuma tuni aka bayar da umurnin fara aikin duba sauran gidajen da ke unguwar domin tabbatar da ingancinsu bayan wannan hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.