Haiti - Ta'addanci

'Yan Colombia 26 da Amurkawa 2 ne suka kashe shugaban Haiti - 'Yan Sanda

Wasu daga cikin gungun sojojin hayar da suka kashe shugaban kasar Haiti Jovenel Moise.
Wasu daga cikin gungun sojojin hayar da suka kashe shugaban kasar Haiti Jovenel Moise. © AP Photo/Joseph Odelyn

Hukumumin tsaron kasar Haiti sun ce wani gungun sojin kundumbala da ya kunshi mutane 28 ne ya kaddamar da harin da ya yi sanadiyyar hallaka shugaban kasar Jovenel Moïse a ranar larabar da ta gabata.

Talla

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar ta ce 26 daga cikin maharan ‘yan kasar Colombia ne sai kuma Amurkawa 2.

Shugaban rundunar ‘yan sandan kasar ta Haita Léon Charles ya ce daga cikin maharan 28 an cafke Amurkawa 2 da kuma 15 ‘yan asalin kasar Colombia tare da gabatar da wasu daga cikinsu gaban manema a yammacin jiya alhamis.

Wasu daga cikin maharan da ake tuhuma da kashe shugaban kasar Haiti Jovenel Moise bayan tsare su a birnin Port-au-Prince.
Wasu daga cikin maharan da ake tuhuma da kashe shugaban kasar Haiti Jovenel Moise bayan tsare su a birnin Port-au-Prince. © AP Photo/Jean Marc Hervé Abélard

Shugaban ‘yan sandan ya ci gaba da cewa an bindige 3 daga cikin maharan dukkaninsu ‘yan kasar Colombia, to sai dai akwai sauran mutane 8 da har yanzu ake ci gaba da farautarsu cikin Port-au-Prince fadar gwamnatin kasar.

Mai magna da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Taiwan Joanne Ou, ta tabbatar da bayanan da ke cewa an kama 11 daga cikin maharan ne a cikin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Port-au-Prince, yayin da ministan tsaron Colombia Diego Molano ya ce 6 daga cikin mutanen da aka cafke lalle tsoffin sojojin kasar ne.

Yayin da aka ci gaba da bincike don gano wadanda ke da hannu a wannan kisa, tuni babban mai shigar da kara na gwamnatin Haiti Bed-Ford Claude ya bai wa ‘yan sandan kasar umurnin ganawa da illahirin jami’an tsaro da ke da alhakin kare lafiyar shugaba Moise don yi masu tambayoyi don sanin ko akwai wata rawar da suk taka a wannan kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.