Amurka-HAITI

Amurka ta yi biris da bukatar Haiti ta neman kariya bayan kisan shugabanta

Marigayi shugaban kasar Hiati Jovenal Moise.
Marigayi shugaban kasar Hiati Jovenal Moise. © AP - Dieu Nalio Chery

Amurka ba ta karbi bukatar da Haiti ta mika mata ta neman dakarun da za su tsare mata mahimman kadarorinta ba, bayan kisan gillar da aka wa shugaban kasar Jovenel Moise, duk  da alkawarin da ta yi na taimakawa wajen bincike.

Talla

Kashe Moise da  wasu ‘yan bindiga suka yi da safiyar Laraba a gidansa da ke birnin Port Au Prince ya sake dulmaya kasar cikin rikicin siyasa da ka iya ta’azara matsalar yunwa da ake fuskanta a kasar, harkar daba da kuma matsalar bullar annobar Covid-19.

Ministan zabe na Haiti Mathias Pierre ya ce firaministan wucin gadi na kasar, Claude Joseph ne ya mika bukatar taimakon dakaru ga Amurka, yana mai cewa Haiti ta kuma nemi kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya taimaka mata da sojoji.

Amma wani babban jami’i a Amurka ya ce babu wani shiri da kasar ke yi na aikewa da dakaru Haiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.