ANNOBAR-KORONA

Macron ya sanar da sabbin matakan yaki da korona

Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron © Élysée

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewar ya zama wajibi ga daukacin jami’an kiwon lafiyar kasar su karbi allurar rigakafin cutar korona domin kare kan su da sauran jama’ar da suke kula da su.

Talla

Yayin jawabi ga al’ummar kasar dangane da muhimmancin karbar allurar rigakafin da kuma wasu matakai domin dakile yadda cutar ke yaduwa, shugaban yace daga watan Satumba mai zuwa za’a fara binciken jami’an kula da lafiyar da kuma masu kula da gidajen tsofaffi.

Wannan ya biyo bayan kin yardar da wasu jami’an kiwon lafiya suka yi su karbi allurar.

Macron yace za’a kara wa’adin amfani da takardar shaidar karbar rigakafin zuwa gidajen cin abinci da na barasa da kuma wasu wuraren taron jama’a.

A karkashin sabon tsarin, duk mai bukatar shiga gidan sayar da abinci ko gidan giya sai ya gabatar da shaidar dake nuna cewar an masa rigakafin cutar, ko kuma yana dauke da takardar shaidar dake nuna cewar baya dauke da ita.

Alamun cutar korona
Alamun cutar korona © 网络照片 Getty Images/iStockphoto - ismagilov

Shugaban yace Faransa na samun karuwar masu harbuwa da cutar korona daga ciki da wajen kasar, inda ya kara da cewar, duk da yake yanayin bai baci ba, rashin daukar matakai masu tsauri zasu sa annobar tayi girma.

A kokarin ganin an dakile karuwar masu harbuwa da cutar, Macron yace zasu fadada allurar rigakafin ga jama’a da kuma hukunta wadanda suka ki karbar ta.

Wannan sanarwa ta nuna sauyin da aka samu akan manufofin gwamnatin kasar wadda a watannin baya ta janye wasu daga cikin matakan da ta dauka domin shawo kan yaduwar cutar.

Alkaluma sun ce masu harbuwa da cutar a Faransa sun kai 4,200 kowacce rana, yayin da ake dauke da mutane 7,000 dake fama da cutar a asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.