Cuba - Zanga-zanga

Jami'an tsaron Cuba sun tsare masu zanga-zangar sama da 100

Yadda jami'an tsaron Cuba suka kame masu zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar, 13-07-21.
Yadda jami'an tsaron Cuba suka kame masu zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar, 13-07-21. YAMIL LAGE AFP

Jami'an Tsaro a kasar Cuba sun kama akalla mutane 100 da suka shiga zanga zanga mafi girma da aka taba gani a kasar domin nuna adawa da gwamnatin mai ci, a daidai lokacin da Amurka da kasashen Turai ke cewa ya dace hukumomin kasar su saurari masu zanga zangar.

Talla

Sanarwar da kungiyar da ta shirya zanga zangar ta gabatar yace yawan mutanen da aka tsare ya kai 130, cikin su harda Jose Daniel Ferrer da Manuel Cuesta Morua, biyu daga cikin fitattun Yan adawa.

Masu zanga Zanga a kasar Cuba dake adawa da gwamnati 11 ga watan Yuli 2021.
Masu zanga Zanga a kasar Cuba dake adawa da gwamnati 11 ga watan Yuli 2021. AP - Daniel A. Varela

Ita ma kungiyar mata masu sanya fararen kaya ta sanar da kama shugabar ta Berta Soler, yayin da Hukumomin Cuba suka zargi Amurka da tinzira zanga zangar.

Ko a baya-bayan nan sai da Cuba ta bayyana matakin Amurka na kuntatawa tattalin arzikinta a matsayin dalilin da ya janyo gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnatin Kwamunisancin kasar, yayin da shugaba Joe Biden ya goyi bayan kirye-kirayen kawo karshen zaluntar al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.