Iran-Amurka

Amurka ta bai wa Iran damar taba kudinta da ta rike

Sabon shugaban Iran, Ebrahim Raisi.
Sabon shugaban Iran, Ebrahim Raisi. AP - Vahid Salemi

Amurka ta baiwa Iran damar yin amfani da kudaden asusunta da aka kulle wajen biyan bashin da kasashen Korea ta kudu da Japan ke binta, dai dai lokacin da tattaunawa ke ci gaba da nisa a kokarin gyara yarjejeniyar nukiliyar kasar don rage mata takunkuman karya tattalin arziki.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta bai wa Kamfanonin Japan da na Korea ta kudu damar karbar kudaden da su ke bin Iran din kai tsaye daga asusun da Amurkan ta kulle mata, kudaden da ke a matsayin na cinikayyar da ta shiga tsakaninsu gabanin dawo da takunkuman da Donald Trump ya yi wa kasar a 2019.

Amurkan wadda ta ci gaba da sanya takunkuman karya tattalin arziki kan Iran game da matakin da ta dauka na ci gaba da fadada ayyukan nukiliyarta da kuma bijire wa wasu dokoki a wancan lokaci, kamfanonin da ke hada-hada da bankunan kasar na fuskantar hukuncin kullewa ko kuma rike musu wani adadi na kudade daga Amurkan.

Kakakin ma’aikatar wajen ta Amurka, ya ruwaito cewa Sakataren wajen kasar Antony Blinken ya sanya hannu kan bukatar daga kafa ga Iran din har na tsawon kwanaki 90 don kammala biyan kasashen kudadensu daga rufaffen asusun ajiyar nata.

Sai dai sanarwar ma’aikatar da ke sanar da matakin ta ce dage kafar da Amurkan ta yi wa Iran ba zai bayar da damar aikewa da ko sisi daga rufaffen asusun ajiyar zuwa ga kasar ba.

A cewar Amurka matakin na da nufin kyautata wa kasashen na Korea ta kudu da Japan wadanda ke a matsayin manyan abokanan Amurkan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.